Bankwana - Abdul Director (Albums 2022)

preview_player
Показать описание
Follow Abdul Director The Follow 👇👇

YouTube

Audiomack

Spotify

SoundCloud

Facebook

Instagram

Twitter

_____
Lyrics

Bani son rabuwa dake Habiba kar kiyi minni bankwana. zuciya ta taki ce Abdul bazan yi miki butulci ba.

1
komai cikin duniyan ga nada sannadi nasa na fahimta.
yau da gobe akwan atashi nasarar mu muke kusanta.
nai godiya agurin ka Allah daka haɗan da gwana ta mata.
Wato Habiba abar yabona da sonta zuci take fusata.
nai fahari ni keda wannan kyakkyawar dole karrama ta.
daure Habiba rike amanar soyayya bama rabe ba.

2
Garin masoyi baya nisa so ne silar da na yada zango.
naje ni har birni na Sokoto domin so bashi ga rago.
a dukka minti so yake gudana ban dubin agogo.
da so da kauna kinyi min Habiba igiyar so na wurgo.
amanar da kika rike gareni dole kaya na nashirgo.
sonki bani da mafita Habiba daure tallafi raina.

3
a sanadinki na gane waye masoyin gaskiya aguna.
Sam baki son dukkan abinda xaya bataminni raina.
cikin nishadi walwala da girmamawa mukewa juna.
dukka bogo na zuciya Habiba sonki yake gudana.
to babu ke a rayuwar nan shin ina zan sanya kaina.
nai kuduri nayi alkawar... barin ki sai baya na raina.

4
inso yakai so sai ya sanya ai kamanni da juna.
da Ni dake munzam guda na zam Hassan ke kuma Hussaina.
a rarrabe mu akwai wuya zan jure sukan makiya na.
ki gane so daina da zarar ya fice to anyi barna.
ki auri wanda yake bidar ki don Allah da rikon amana.
na tabbata dukkan farin ciki zaki samu agurina.

5
wallah kin mini karrama na yarda so ke zamma kauna.
na gaskata tunda ankace ido mudu har zuciya na.
riba ta soyayya ayo aure kar a rabe da juna.
soyayya ta gaskiya muke ciki nata ba hiyana.
kiyi alkawar na zama dani har abada a dare da rana.
karbi furen so Habiba rabin jiki kedai a raina.

6
bissalam masoyi gareki nan ne zanyi bankwana.
wannan ki dauka wasika ce gunki domin farin ciki na.
sai dake rayuwa zatai mini daidai hankali na.
mai son rabamu yai hakuri Habiba Abdul dai ta nuna.
ba yaudara Allah yana kallo acikin lamura na.
rintsi wuya duka zana jure, Habiba kece Mahadina.

Bani son rabuwa dake Habiba kar kiyi minni bankwana. zuciya ta taki ce Abdul bazan yi miki butulci ba.

#abduldirector #hausamusic #nuraminuwa
Рекомендации по теме
join shbcf.ru